Sunday, 24 April 2016

za'a fara dawo da yan majalisar dattawadattawa dana wakilaiwakilai gida.



Don sayen naurar computer cikin sauki danna wannan hoton na kasa





Za A Fara Dawo Da 'Yan Majalissar Dattawa Da Na Wakilai Gida Saboda Kuncin Rayuwa Da Suka Jefa Talakan Nijeriya

Daga Bashir Abdullahi El-Bash

Wasu gungun kungiyoyin farar hula wanda suka nemi a saka ye sunan su saboda su cimma burin su na ceto Nijeriya, sun yi kira da a fara daukar matakai na dawo da 'yan majalissar dattawa da na wakilai gida daga Abuja domin ladabtar da su saboda kuncin rayuwa da suka jefa talakan Nijeriya ciki.

Wannan sanarwa ta fito ne daga bakin shugabannin kungiyoyin su kimanin 200 wanda suke gudanar da taro na kwana 3 a jihar Katsina, taron da aka fara a ranar Juma'ar da ta gabata, kuma za'a kare shi a yau Lahadi.

Yanzu haka akwai mazabu kusan 10 da suka gama shirin dawo da wakilan nasu daga Abuja tsakanin jihar Kano da Katsina da kuma Zamfara. Kungiyoyin sun buga wasu takardu wanda za'a raba a masallatai coci- coci da kasuwanni da duk inda jama'a suke taruwa domin cimma burin su. Sun ce dawo da wakilan nasu ya zama dole saboda irin yadda suke ta yi wa shugaban kasa Buhari zagon kasa a yunkurin sa na inganta rayuwar talakan Nijeriya.

Bayan haka sun yi kira ga sauran kungiyoyi masu zaman kansu da su hada kai da su domin dawo da duk wani azzalumin wakilin jama'a da ba ya kaunar cire talaka cikin kuncin rayuwa da yake ciki, sannan hadakar kungiyoyin sun ce babu sani babu sabo a wannan kuduri nasu.

A karshe shugabannin kungiyoyin sun ce suna bukatar duk dan Nijeriya mai kishi da ya ga wannan sanarwa ya rubuta sunan mai wakiltar su a matakin tarrayya da yankin da yake wakilta da sunan mazabar sa domin buga wata jarida mai dauke da sunayen wakilan.

No comments:

Post a Comment